Isa ga babban shafi
Habasha

Zabtarewar bola ta yi ajalin mutane kusan 50 a Addis Ababa

Akalla mutane kusan 50 suka kwanta dama, da dama kuma suka jikkata sakamakon zabtarewar bola da ta auku a inda ake zub da shara a wajen birnin Addis Ababa na Habasha.

Wasu da aka ceto a zabtarewar kasa da ya auku a Habasha
Wasu da aka ceto a zabtarewar kasa da ya auku a Habasha REUTERS/Stringer
Talla

Kamfanin dilancin labaran faransa AFP ya rawaito cewa akasarin wadanda abin ya shafa marasa galihune da ke rayuwa a kusa da inda ake zub da shara.

Jami’in sadarwar Yankin, Dagmawit Moges yace mata 32 da maza 14 suka mutu a hadarin, kuma akasarin su wadanda suke tone sharar ce suna neman abinda zasu sayar su sa a bakin salati.

Yankin Koshe inda lamarin ya auku, ya kasance baban juji a Addis Ababa sama da shekaru 40, kuma akwai mutane kusan miliyan 4 da ke rayuwa a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.