Isa ga babban shafi
Sudan

Shugaba El Beshir zai halarci taron Larabawa a Jordan

Kungiyar Kare Hakin Bil Adama ta Human Rights Watch ta bukaci hukumomin kasar Jordan da su hana shugaban kasar Sudan Omar Hassan Al Bashir shiga kasar ko kuma su kama shi kan zargin laifufukan yaki a Darfur.

Shugaban kasar Sudan Omar El Bechir a wani taron kasashen Larabawa a Abou Da
Shugaban kasar Sudan Omar El Bechir a wani taron kasashen Larabawa a Abou Da REUTERS/Stringer
Talla

Elise Keppler, Daraktan kungiyar ya ce barin shugaba El Bashir ya shiga kasar babban laifi ne saboda yadda kotun Duniya ke neman sa ruwa a jallo.

Shugaban na Sudan na daya daga cikin wadanda aka gayyata wajen taron shugabannin kungiyar kasashen Larabawa da za’a gudanar ranar laraba a Jordan.

Wasu kasashen a baya sun baiwa shugaban na Sudan damar  sauka cikinsu ba tareda  ya fuskanci matsalla ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.