Ahmed Kathrada na Afrika ta kudu ya rasu
Daya daga cikin shugabannin yaki da mulkin wariyar launin fata a Afirka ta kudu Ahmed Kathrada kuma makusanci ga Nelson Mandela ya rasu yana da shekaru 87 a duniya.
Wallafawa ranar:
Kathrada na daga cikin wadanda aka daure a shekarar 1964 tare da Mandela, shari’ar da ta janyo hankalin kasashen duniya zamanin mulkin wariyar launin fata a Afrika ta kudu
Kathrada ya kwashe shekaru 26 da watanni 3 a daure, kuma ya yi shekaru 18 a gidan yarin Robben Island.
Bayan kawo karshen mulkin wariya, Kathrada ya taba zama mai ma Mandela shawara kan harakokin majalisa daga shekarar 1994 zuwa 1999.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu