rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar Zaben Nijar

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ba zan sauya kundin tsarin mulki ba-Issoufou

media
Shugaban Jamhuriyar Nijar Issoufou Mahamadou

Shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou ya ce babu abinda zai sa shi sauya kundin tsarin mulkin kasar dan neman wa’adi na uku bayan karewar wa’adinsa a shekarar 2021.


Yayin da yake amsa tambayoyi kan cikar sa shekara guda a karagar mulki, shugaban ya ce burin sa shirya karbaben zabe da duniya za ta amince da shi a shekarar 2021.

Shugaba Issofou ya ce shi cikkaken mai bin tafarkin demokradiya ne, saboda haka ba zai dauki kan sa a matsayin wanda babu wanda zai iya maye gurbin sa ba.

Idan ya samu nasarar kamala wa’adin sa, shugaban zai zama na farko a tarihin Nijar da zai mika mulki ga wani shugaban kasa ta hanyar zabe.
Elhj Dudu Rahama daga bangaren Adawa ya bayyana cewa sun sa ido a kai.