Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Afrika ta Kudu ba ta saba doka don kin kama shugaban Sudan ba

Gwamnatin Afirka ta Kudu da ke bayar da shaida a wannan juma’a gaban wakilan Kotun Duniya da ke zama na musamman a birnin Pretoria, ta ce ba inda kasar ta saba doka domin ta ki kamawa tare da mika shugaban Sudan Umar Hassan Albashir a gaban kotun lokacin da ya ziyarci kasar shekaru biyu da suka gabata.

Shugaban Africa ta Kudu Jacob Zuma tare da Omar al-Bashir Shugaban kasar Sudan
Shugaban Africa ta Kudu Jacob Zuma tare da Omar al-Bashir Shugaban kasar Sudan
Talla

Dire Tladi, babban lauyan gwamnatin Afirka ta Kudu, ya ce ba wata doka da ke tilasta wa kasar yin amfani da karfi domin kama shugaban wata kasa har ma a gurfanar da shi a gaban kotu.

A shekara ta 2015 lokacin  taron Kungiyar Tarayyar Afirka, kotun da ke Hague ta bukaci a kama Albashir wanda ke daya daga cikin shugabannin kasashen Afirka da suka halarci taron domin cajin sa da aikata laifufukan yaki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.