rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Mali ECOWAS CEDEAO

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Masu Jihadi a Kasar Mali Sun Kashe Mutane 5

media
Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita. Pierre Rene-Worms/RFI

Mayaka masu ikirarin jihadi a kasar Mali sun kai wani kazamin hari tsakiyar kasar a yau Asabar inda suka kashe mutane  5, mako daya bayan da aka kira wani taro na kasa don neman zaman lafiya da ‘yan tawaye dake Arewacin kasar.


Wani mai Magana da yawun wata kungiyar  Justice in Azawad mai suna Oumar Ag Keling ya shaidawa kamfanin Dillancin labaran Faransa, AFP  cewa sun kashe masu  mutane 4 da kuna Hakimin garin na Gargando mai kimanin nisan kilomita 170 yammacin garin nan mai tarihi Timbuktu.

Majiyoyin Sojan Mali sun gaskata wannan hari na yau.