rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Masar Vatican

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ziyarar Fafaroma na nan zuwa Masar

media
Shugaban mabiya darikar Katolika Fafaroma Francis REUTERS/Alessandro Bianchi/File Photo

Shugaban mabiya Darikar Katolika Fafaroma Francis ya ce ziyararsa na nan zuwa Masar kamar yadda aka tsara a karshen watan Afrilu duk da munanan hare haren da aka kai wuraren ibadar kiristoci a karshen mako inda mutane 44 suka mutu.


Fafaroma zai kai ziyara Al Kahira ne a ranakun 28 zuwa 29 na Afrilu domin tattaunawa da babban limamin masallacin Azhar Sheikh Ahmed al-Tayeb a babban taron Musulmi da Kiristoci.

Wannan na zuwa a yayin da gwamnatin Masar ta kafa dokar ta-baci ta watanni uku bayan munanan hare haren bama bamai da aka wuraren ibadar Kiristoci a Tanta da Alexandria. Kungiyar IS ta fito ta yi ikirarin daukar alhakin harin.

Babban limamin mabiya Katolika a Faransa Jean-Louis Tauran kuma babban mai da’awar tabbatar da fahimtar juna tsakanin Kiristoci da musulmi ya tabbatarwa manema labarai cewa ziyarar Fafaroma na nan zuwa Masar kamar yadda aka tsara.

“Yadda na san Fafaroma, na tabbata zai kai ziyara Masar saboda taron musulmi da Kirista da aka shirya a jami’ar Al Azhar tare da kai wa kiristoci ziyara da ke cikin mawuyacin hali”, a cewar Tauran.

Tauran ya ce sakon Fafaroma shi ne tabbatar zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kirista domin a cewarsa duk masu imani yan kasa ne da za su tabbatar da dabi’unsu na kwarai a doron kasa.