Isa ga babban shafi
Afrika-tafkin Chadi-Najeriya

Ruwan tafkin Chadi ya ragu da kashi 90 - FAO

Hukumar lura da samar abinci ta Majalisar dinkin duniya FAO, ta ce kusan mutane milyan 7 ne ke cikin hadarin fuskantar yunwa a yankin tafkin Chadi.

Daraktan hukumar kula da samar da abinci ta majalisar dinkin duniya FAO, Graziano Da Silva, yayin ziyarar da ya kai jihar Borno ranar 7 ga watan Afrilu na shekarar 2017.
Daraktan hukumar kula da samar da abinci ta majalisar dinkin duniya FAO, Graziano Da Silva, yayin ziyarar da ya kai jihar Borno ranar 7 ga watan Afrilu na shekarar 2017. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Kasashen da lamarin ya shafa kamar yadda hukumar ta bayyana sun hada da Kamaru, Nijar, arewa maso gabashin Najeriya da kuma ita kanta kasar Chadi.

Daraktan hukumar bunkasa ayyukan noma na hukumar ta FAO José Graziano da Silva, wanda ya kammala ziyara a kasar ta Chadi da kuma wani bangare na arewacin Najeriya, ya ce daga shekara ta 1963 zuwa yanzu, ruwan tafkin Chadi ya ragu da kashi 90, lamarin da ya haifar da barazanar yunwa a yankin da a baya ya dogara kan noman rani da sana’ar kamun kifi wajen rayuwa.

Da Silva ya kara da cewa daya daga cikin manyan dalilan da suka haddasa mutanen yankin shiga cikin matsi, shi ne yadda jama’a ke dada tururuwa zuwa yankin na tafkin Chadi sakamakon rikicin Boko Haram da raba miliyoyin mutane da muhallansu, musamman daga arewa maso gabashin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.