Isa ga babban shafi
Sudan ta kudu

An kashe ma’aikatan MDD 3 a Sudan ta Kudu

Kungiyar samar da abinci ta duniya WFP ta yi allah-wadai da kisan da aka yi wa wasu ma’aikatanta a kasar Sudan ta Kudu yayin da suke gudanar da ayyukansu a yankin Wau gari na biyu mafi girma a kasar.

jami'an Hukumar Samar da abinci ta duniya uku aka kashe a Sudan ta Kudu
jami'an Hukumar Samar da abinci ta duniya uku aka kashe a Sudan ta Kudu Filip Warwick
Talla

A ranar lahadin da ta gabata ne dai wasu suka yi wa fararen hula su 16 kwanton bauna suka kuma kashe su.

Kungiyar Samar da abinci ta duniya ta ce ma’aikatan Majalisar sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suke kokarin isa ga runbunan abincin da aka tanadarwa mabukata a kasar.

Yakin Sudan ta Kudu na sama da shekaru biyu ya yi sanadiyar rayukan mutane fiye da dubu daya baya ga wasu miliyoyi da yanzu haka ke fuskantar matsalar karancin abinci da aka ce shine mafi muni a tsawon shekaru.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.