Sojojin Kenya sun kashe mayakan al-Shebab 52
Rundunar tsaron Kenya ta kashe mayakan al-Shebab 52 a wani harin konton bauna da ta kai musu a sansaninsu da ke kudsancin Somalia.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Mai magana da yawun rundunar sojin kasar Kanar Joseph Owuoth ya ce, lamarin ya auku ne a yankin Badhaadhe da ke Low Juba.
Kanar Owuoth ya ce, sojojin da suka kai farmakin sun gano manyan bindigogi da kayayyakin kera bama-bamai na mayakan al-Shebab.
Kasar Kenya na da dubban dakaru a rundunar hadaka ta kungiyar kasashen Afrika da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Somalia mai fama da barazanar tsaro saboda ayyukan ta'addancin al-Shebab.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu