Isa ga babban shafi
Najeriya

Biafra: Kotu ta bada belin Nnamdi Kanu

Wata babbar Kotu a birnin Abuja da ke Najeriya ta bayar da belin Nnamdi Kanu daya daga cikin shugabannin masu fafutukan kafar kasar Biafra bisa dalilai na rashin lafiya.

Nnamdi Kanu, daya daga cikin shugabannin masu fafutikar kafa kasar Biafra a Najeriya
Nnamdi Kanu, daya daga cikin shugabannin masu fafutikar kafa kasar Biafra a Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

An bayar da belin Kanu ne da sharadin gabatar da mutane uku da kowanne ya mallaki dukiyar da ta kai Naira milyan 100, kuma su mutanen uku su kasance Sanata Guda, Shugaban Addinin yahuda da Nnamdi ya ce shi ne Addininsa da kuma wani fitaccen mutun zaunane kuma mai kadara a Abuja.

Sannan kotun ta haramta wa Kanu halartar duk wani gangami da adadin mahalartansa ya wuce mutane 10 da kuma tattaunawa da kafar yada labarai.

A watan Oktoban 2015 ne aka kama Kanu da ke jagorantar kungiyar fafutikar kafa kasar Biafra IPOB tare da watsa farfaganda a wata kafar rediyo da ya ude a London.

Laifukan da ake tukumar Kanu sun hada da cin amanar kasa.

Bayan da belinsa na zuwa a yayin da ya rage kwanaki a cika shekaru 50 da ikirarin kaddamar da ‘yancin Biafra, al’amarin da ya jefa Najeriya cikin yakin basasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.