Isa ga babban shafi
Ghana

Ghana za ta bullo da shirin ilimi kyauta ga ‘Yan Sakandare

Ghana na shirin kaddamar da shirin samar da ilimi kyauta ga daliban makarantun Sakandare wanda zai shafi kowa, da ake ganin zai sauya rayuwar miliyoyan ‘ya’yan marasa karfi musamman mata a kasar.

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo
Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo REUTERS/Luc Gnago
Talla

Shirin na cikin alkawullan da shugaban kasar Nana Akufo-Addo ya yi a lokacin da ya ke yakin neman zabensa.

Matasa dai na fuskantar kalubalen samun shiga manyan makarantun sakandare, saboda tsada da yawan mabukata musamman yadda sai dalibi ya ci jarabawa kafin ya samu shiga makarantun.

Gwamnatin kasar ta ce manufar shirin shi ne karfafawa ilimin ‘yaya mata domin ci gaban kasar.

Wasu alkalumman Majalisar Dinkin Duniya sun ce Maza sun zarce Mata yawa a makarantun Ghana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.