rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Mali ECOWAS CEDEAO

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Hukumomi a Mali Sun Kara Tsawaita Dokar Ta Baci da Watanni Shida

media
Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita. rfi

Majalisar Dokokin kasar Mali ta tsawaita dokar ta baci da karin watanni shida a kokarinta na yakar masu tsatstsaurar ra'ayin addinin Islama dake kai hare-hare a yankunan dake arewaci kasar Mali.


Shugaban Hukumar Shari'a ta majalisar Zoumana N’dji Doumbia ya fadi cewa an karawa Dakarun kasar karfi iko don kamawa da tsare wadanda ake tuhuma da tsatstsaurar ra'ayi.

A watan 11 na shekara ta 2015 aka kafa dokar ta bacin na farko bayan da aka lura da tabarbarewar tsaro saboda barazanar masu tsananin kishin Islaman.