Isa ga babban shafi
Najeriya

Sule Lamido zai ci gaba da zama a gidan yari

Wata Kotu a Jigawa ta bayar da umurnin a ci gaba da tsare tsohon gwamnan Jihar Sule Lamido a gidan yari har zuwa ranar 4 ga Mayu da za ta saurari bukatar bayar da shi beli kamar yadda lauyoyin da ke kare shi suka bukata.

Kotu ta ki bada belin Sule Lamido tsohon gwamnan Jigawa
Kotu ta ki bada belin Sule Lamido tsohon gwamnan Jigawa RFIHausa/Dandago
Talla

Kotun ta Majistire ta ce tana bukatar lokaci domin nazari kan karar da aka shigar gabanta kafin ta bayar da belin tsoho gwamnan.

Lauyoyin gwamnati ne suka yi watsi da bukatar bayar da belin Sule Lamido, lamarin da ya haifar da barkewar zanga-zanga daga bangaren magoya bayan tsohon gwamnan.

Ana tuhumar tsohon gwamnan na Jigawa da aikata laifuka guda hudu da suka shafi tayar da hankalin jama’a da rikici a jihar, zargin da Sule Lamido ya musanta.

A ranar Lahadi ne ‘Yan sanda suka cafke Sule Lamido a Kano tare da yin binciken kwa-kwaf a gidajensa da ke Kano da Jigawa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.