Isa ga babban shafi
Liberia

Sabuwar cuta da ke kisa ta bula a Liberia

Mutane na ci gaba mutuwa a Liberia sakamakon wata cuta da aka kasa fahimta kuma da ke ci gaba yaduwa a sassan kasar.

Shugaban kasar Liberia Ellen Johnson Sirleaf
Shugaban kasar Liberia Ellen Johnson Sirleaf REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Hukumomin lafiya a Liberia sun tabbatar da mutuwar mutane 12 bayan cutar ta bulla a Manrovia babban birnin kasar.

Cutar da ta zama annoba ta shigo har cikin Monrovia, bayan rasuwar wani mutum da ya halarci bikin jana’iza a babban birnin kasar daga Sinoa.

Hukumar Lafiya WHO da ma’aikatar lafiya ta Liberia sun ce mutumin ya nuna wasu alamu da ba a tantance ba kafin ya mutu.

Kuma yanzu shi ne mutum na 12 da ya rasu sakamakon cutar da ba a san kanta ba wacce ta fara kisa cikin mako guda a Liberia.

Cutar ta fara bulla ne kudu maso gabashin Liberia a wani bikin jana’izar wani shugaban addini a yankin Sinoa.

WHO ta ce cutar ba ta da nasaba ko yanayi da cutar Ebola da ta kashe dubban mutane a kasar. Haka ma cutar ba ta da yanayi da cutar Lassa.

Alamun cutar kuma sun hada da zazzabi mai karfi da ciwon kai da amai da gudawa

Yanzu haka ana gudanar da gwaje-gwaje a kasashen waje domin gano cutar da kuma hanyoyin magance ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.