CAR
‘Yan bindiga sun hallaka mutane 45 a Afirka ta Tsakiya
Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama ta Human Rights Watch ta bayyana cewar kungiyoyin ‘yan bindiga dadi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun hallaka mutane akalla 45 a matsayin daukar fan sa a cikin watanni uku da suka gabata.
Wallafawa ranar:
Talla
Lewis Mudge, Jami’in Hukumar da ke gudanar da bincike a Afirka ya ce ganin yadda bangarorin Anti Balaka da Seleka ke yakar juna dan samun iko, fararen hula na ci gaba da dandana kudar su a kasar.
Rikici a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ya barke ne tun a shekarar 2013 lokacin da aka kifar da gwamnatin shugaba Francois Bozize.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu