Somalia na bincike kisan Minista akan kuskure
Shugaban Kasar Somalia Mohammed Abdullahi Farmajo ya bukaci gudanar da bincike kan yadda jami’an tsaro suka harbe matashin ministan ayyuka Abbas Abdullahi Siraji mai shekaru 31 bisa kuskure.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Shugaban wanda ya katse ziyarar da ya ke yi a kasar Habasha, ya ce sun kadu da kisan saboda haka za su tabbatar an hukunta duk wanda ya ke da hannu a kisan.
Rahotanni sun ce masu tsaron fadar shugaban ne suka budewa motar ministan wuta mai suna Abbas Abdullahi Siraji da ke tuka kansa bisa tunanin ‘yan ta’adda ne.
Saboda barazanar mayakan Al Shebaab a Somalia yana da wahala Jami’in gwamnati ya fito kan titi a Mogadishu yana tuka kansa ba tare da jami’an tsaron ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu