rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Sudan ta Kudu Ta'addanci Hakkin Dan Adam

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Yara 'yan gudun hijira daga Sudan ta Kudu sun haura miliyan 1

media
Mata da kananan yara 'yan gudun hijira da ke jiran a raba musu abinci karkashin jagorancin jami'an majalisar dinkin duniya na hukumar samar da abinci ta Duniya (WFP) a yankin Thonyor, da ke jihar Leer a Sudan ta Kudu a ranar, 26, ga watan Fabarairun 2017. REUTERS/Siegfried Modola

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yakin da ake cigaba da gwabzawa a kasar Sudan ta Kudu, ya tilastawa kananan yara sama da miliyan daya tserewa daga kasar, yayinda kuma wasu yaran miliyan daya da dubu 400, ke cigaba da rayuwa a sansanonin ′yan gudun hijira da ke kasar.


Rahoton hukumar lura da yara da kuma bunkasa al:adu ta majalisar dinkin duniyar ya ce kasha 62 daga cikin mutane miliyan da dubu 800 da yaki ya tilastawa tserewa zuwa kasashen da ke makwabtaka da sudan ta kudu kananan yara ne.

Kasashen da `yan gudun hijirar mafi yawansu kananan yara suka tsere sun hada da Habasha, Kenya da kuma Uganda.

Wata mai Magana da yawun Hukumar UNICEF Leila Pakkala, ta ce hadarin da kananan yaran ke fuskanta ba wai ya tsaya bane kan rabasu da muhallansu da kuma cin zarafi, a gefe guda mayakan `yan tawaye na cigaba da tilastawa kananan yaran shiga yakin da ake gwabzawa tsakanin sojin sudan ta kusun da `yan tawaye.

A shekara ta 2011 ne dai Sudan ta Kudu ta samu 'yancin kai daga kasar Sudan, sai dai bayan shekaru biyu, sabon fada ya barke a kasar, sakamakon zargin da shugaba Salva Kirr ya yiwa mataimakinsa a waccan lokacin Riek machar na yunkurin yi masa juyin mulki.

Zargin ya haifar da mummunan fada tsakanin sojoji masu biyayya ga machar da sojin gwamnati, fadan da sannu a hankali ya juye zuwa na kabilanci, wanda ya kara ta`azzara halin yunwa saboda karancin abinci da al’ummar kasar Sudan ta Kudun ke fuskanta.

Zuwa yanzu dai bincike ya nuna cewa sama da kananan yara dubu 1 ne aka hallaka sakamakon yakin da ske cigaba da gwabzawa a kasar.