Isa ga babban shafi
Somalia

Somalia ta nemi taimakon duniya

Shugaban Somalia Mohamed Abdullahi Mohamed Farmajo ya yi kira ga kasashen duniya su taimakawa kasar shi yakar ta’addaci da talauci, a wani babban taro da aka gudanar a yau a London kan yadda za a tallafawa kasar.

Firaministar Birtaniya Theresa May ta jagoranci taron Somalia a Lancaster
Firaministar Birtaniya Theresa May ta jagoranci taron Somalia a Lancaster REUTERS/Jack Hill/Pool
Talla

Taron ya fi mayar da hankali ga matsalar tsaro da fari da kuma yadda za a farfado da tattalin arzikin Somalia, inda rabin ‘yan kasar ke fama da yunwa.

Shugaba Farmajo na Somalia ya shaidawa taron London cewa kasarsa na iya farfadowa ga kasuwancin da aka santa a baya idan har za a yaki barazanar fari da fashin teku da kuma ta’addanci.

An shirya taron ne na kwana guda a London da ya samu halartar shugabannin wasu kasashen duniya kan yadda za a taimakawa Somalia a fannin tsaro ci gaba da kuma tattalin arziki zuwa 2020.

Farmajo ne ya jagoranci taron tare da sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da kuma Firaministan Birtaniya Theresa May.

Guterres ya shaidawa taron cewa Somalia na bukatar tallafin kudi kimanin dala miliyan 900 kafin karshen shekarar nan domin magance matsalar fari da ya kira babbar bukatar Somalia.

Sama da mutane miliyan 6 aka bayyana ke bukatar agaji a Somalia wato kusan rabin ‘yan kasar.

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce za a samu yara miliyan 1.4 masu tamowa a bana.

Sannan taron zai tattauna yadda za a taimakawa Somalia da Karin dakarun Afrika domin wanzar da zaman lafiya daga barzanar al Shebaab da ke addabar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.