rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Ebola

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Cutar Ebola ta sake bulla a Jamhuriyar Congo

media
Ebola resurfaces in DR Congo congovoice.org

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta sanar da sake barkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyar Congo a wannan Juma’a.


Hukumar ta ce, kawo yanzu mutun guda ya rasa ransa bayan kamuwa da kwayar cutar a yankin arewa maso gabashin kasar.

Karo na karshe da aka samu barkewar cutar Ebola a Jamhuriyyar Congo shi ne a shekara ta 2014, inda akalla mutane 40 suka rasa rayukansu.

Fiye da mutane dubu 11 ne suka gamu da ajalinsu sakamakon kamuwa da wannan cuta tsakanin shekarar 2014 zuwa ta 2015 a yankin yammacin Afrika, musamman a kasashen Guinea da Saliyo da kuma Laberiya.