Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo

Wasu mutane biyu sun sake kamuwa da cutar Ebola a Congo

Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta ce an sake gano Karin mutane biyu da suka kamu cutar Ebola, a jamhuriyyar Dimokaradiyyar Congo, kwana guda bayanda hukumar ta yi shelar sake bullar cutar a kasar.

Mutane biyu sun sake kamuwa da cutar Ebola a Jamhuriyar Congo.
Mutane biyu sun sake kamuwa da cutar Ebola a Jamhuriyar Congo. appsforpcdaily.com
Talla

Hukumar ta WHO ta ce an gano jimillar mutane 11 kenan da suka harbu da annobar, ciki har da mutane 3 da suka mutu bayan kamuwarsu a garin Likati da ke lardin Bas Uele a arewacin kasar ta jamhuriyar Congo.

Jami’an lafiya sun ce mutun na farko ya kamu da cutar Ebola ne, a ranar 22 ga watan Afrilun da ya gabata.

Sau bakwai jamhuriyyar Dimokaradiyyar Congo ta yi fama da barkewar annobar cutar a baya, kuma na karshe shi ne wanda ya auku a shekara ta 2014.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.