rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar Lafiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sankarau ya kashe mutane 180 a Nijar

media
Cutar Sankarau ta kashe mutane a Nijar da Najeriya youtube

Wasu alkalumman Majalisar Dinkin Duniya sun ce kusan mutane 180 suka mutu sakamakon cutar Sankarau daga watan Fabrairun bana, yayin da kusan 3,000 suka kamu da cutar a sassan kasar.


Rahoton na OCHA hukumar kula da ayyukan jin-kai ta Majalisar Dinkin Duniya ya ce tsakanin watan Janairu zuwa Mayu, kimanin mutane 3,037 suka kamu da cutar.

Rahoton kuma ya ce adadin mutane 179 Sankarau ya kashe a Nijar daga Janairu zuwa Mayu.

Cutar ta fi yin kamari a yankunan kudanci da yammacin Nijar, kuma rahoton ya ce har yanzu ana fama da Sankarau a yankin Maradi.

A bana cutar Sankarau ta kashe mutane sama da 1,000 a Najeriya yayin da mutane kusan 14,000 suka kamu da cutar musamman a arewacin kasar.