Bakonmu a Yau
Auwal Musa Rafsanjani kan matsalar rashawa a sha’anin tsaron Najeriya
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:05
Wani rahoto da Transparency International ta fitar a wannan Alhamis, ya ce matsalar cin hanci da rashawa tsakanin jami’an sojin Najeriya na kawo cikas a kokarin gwamnatin wajen kakkabe mayakan Boko Haram baki daya. Rahoton ya zargi sojojin da azurta kansu ta hanyar kirkirar kwangiloli na bogi da sunan yaki da kungiyar Boko Haram. Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna da daya daga cikin jami’an Transparency International a Najeriya, Auwal Musa Rafsanjani