rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Ebola Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ebola na barazana a Congo

media
WHO ta sanar da sake bullar Ebola a Congo appsforpcdaily.com

Hukumar Lafiya ta duniya WHO ta ce za ta fara gudanar da gwajin rigakafin cutar Ebola da ta sake barkewa a Jamhuriyyar Dimokuradiyar Congo. Cutar ta sake bulla ne a garin Likati inda ta kashe mutane uku, sannan kusan 20 ake zargin sun kamu da cutar.


Har yanzu dai babu wata rigakafin da aka samar domin warkar da Ebola. Amma WHO na son gwajin wata rigakafi ne da wani kamfanin magani na Amurka ya samar idan gwamnatin Congo ta amince.

An taba yin gwajin rigakafin a Guinea daya daga cikin kasashen da suka yi fama Ebola.

Babban Jami’in hukumar lafiya ta WHO a Congo Peter Salama ya ce sun kamala shirye-shiryen gwajin rigakafin a kasar.

Ebola ta sake bulla ne yankin Likati a watan Afrilu, karo na farko tun kawar da cutar a watan Janairun bara bayan ta kashe mutane sama da 11,300.