rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Mali Emmanuel Macron Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Macron na ziyarar farko a Afrika

media
Faransa na da dakaru sama da 1,500 da ke yakar 'yan ta'ada a Mali © Anthony Fouchard/RFI

Shugaban Faransa Emmanuel Macron na ziyararsa ta farko a yankin Afrika tun bayan darewa kan karagar mulki, in da zai yada zango a Mali a yau Juma’a domin ganawa da sojojin Faransa da ke yaki da ‘yan ta’adda.


Shugaba Macron mai shekaru 39 zai gana da dakarun Faransa a yankin Gao a arewacin Mali mai fama da rikicin ‘yan tawaye da ‘yan ta’adda.

Faransa na da yawan dakaru kimanin 1,600 da ke yaki a Mali.

Rahotanni sun ce, tuni Mista Macron ya tattauna da wasu sojojin kasar ta wayar tarho bayan sun samu rauni a fafatawar da suke yi da masu tayar da kayar baya a yankin Sahel.

Kawo yanzu dai babu tabbacin ko Macron zai gana da mahukuntan Mali.

Shekaru hudu ke nan da ’yan ta’adda ke tada kayar baya a arewacin Mali, yayin da sojojin Faransa 19 suka rasa rayukansu tun bayan fara aikin kakkabe mayakan a shekarar 2013.