Isa ga babban shafi
Kano

An yi Jana’izar uwar gidan Malam Aminu Kano

An gudanar da Jana'izar uwar Gidan Malam Aminu Kano, Hajiya Shatu a yau Litinin wadda ta rasu bayan fama da doguwar jinya a birnin Kano. Marigayiya Shatu Aminu Kano ta rasu tana da shekaru 89 a duniya.

An yi jana'izar uwar gidan Malam Aminu Kano, Hajiya Shatu
An yi jana'izar uwar gidan Malam Aminu Kano, Hajiya Shatu RFIHAUSA/DANGAMBO
Talla

Marigayiyar Shatu Aminu Kano ta rasu ta bar jikoki 15.

Ta rasu bayan shekaru 34 da rasuwar mijinta Malam Aminu Kano fitaccen dan siyasa a arewacin Najeriya wanda ya kafa jam’iyyar NEPU ta masu ra’ayin rikau.

Tsohon shugabannin hukumar Zaben Najeriya INEC Farfesa Attahiru Jega ya bayyana marigayiyar a matsayin mace mai kamar maza.‎

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.