Ana zargin Jammeh da sace Dala miliyan 50 a Gambia
Ministan shari’ar Gambia, Abubacarr Tambadou ya zargi tsohon shugaban kasar da sace kudin da ya kai Dala miliyan 50 ta hannun kamfanin sadarwar kasar, yayin da kotu ta sanya takunkumi kan kadarorinsa.
Wallafawa ranar:
Ministan ya ce shugaba Jammeh da kansa ya bada umurnin janye kudaden daga asusun ajiyar kasar da ke Babban Bankin Gambia.
Tambadou ya ce sun yi nasarar samun umurnin kotu na rufe asusun ajiyar tsohon shugaban da kuma kadarorin da ya mallaka tare da kamfanonin da ya ke da alaka da su.
Jami’in ya ce umurnin ya shafi asusun ajiyar bankuna 88 da aka bude da sunan tsohon shugaban da kuma na kusa da shi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu