Isa ga babban shafi
Kamaru

Kamaru ta dora laifin hatsarin jirgin kasa akan Kamfanin Camrail

Wani rahoto da gwamatin Kamaru ta fitar, ya dora alhakin hatsarin jirgin kasar da ya kashe mutane 79 a cikin watan Oktoban bara, kan kamfanin Camrail da ke kula da zirga-zirgar jiragen kasa a kasar.

A ranar 21ga watan Oktoban bara Jirgin kasa ya yi hatsari a Eseka, kasar Kamaru
A ranar 21ga watan Oktoban bara Jirgin kasa ya yi hatsari a Eseka, kasar Kamaru STRINGER / AFP
Talla

Rahoton ya ce, gudun jirgin ya wuce kima duk da matsalar birki da ya ke fama da ita, da kuma lodin kayan da ya fi karfinsa.

Jirgin kasan da ya yi hatsari mallakin kamfanin Camrail ne da ya kasance rukunin kamfanin Faransa na Bollore, wanda ya kauce layinsa a garin Eseke bayan ya baro birnin Younde da nufin isa Douala.

Sanarwar da fadar gwamnatin Kamaru ta fitar, ta ce shugaba Paul Biya ya mayar da hankali kan rahoton, inda zai sake nazarin yarjejeniyar da gwamnati ta amince da kamfanin.

Kawo yanzu dai masu Magana da yawun Bollore a birnin Paris da kuma Camrail a birnin Younde duk sun ki cewa komai kan wannan rahoto.

Kwamitin binciken hatsarin ya ce, taragon jirgin sun kife ne saboda gudun kilomita 96 a cikin sa’a guda da ya yi, a maimakon gudun kilomita 40 a cikin sa’a guda.

Jim kadan da aukuwar hatsarin, alkalumman gwamnati sun nuna cewa, mutane 79 ne suka mutu yayin da fiye da 400 suka jikkata.

Tuni dai iyalan mamatan suka shigar da karar kamfanin Camrail da Bollore a kotu bisa zargin su da yin sakaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.