Isa ga babban shafi
Kamaru

Amnesty ta soki Kamaru kan hakkin dalibai

Kungiyar Amnesty International ta yi Allah wadai da hukumomin kasar Kamaru kan yadda suka ki sakin wasu dalibai 3 da aka yankewa hukuncin daurin shekaru 10 saboda shaguben da suka yi kan kungiyar Boko Haram.

Jami'an kungiyar Amnesty International
Jami'an kungiyar Amnesty International RONALDO SCHEMIDT / AFP
Talla

Kungiyar ta ce ta samu sanya hannu da wasikun mutane 310,000 domin ganin shugaba Paul Biya ya saki daliban, amma sai ‘yan sanda suka mamaye Otel din da suka shirya ganawa da manema labarai domin ganin sun gabatar da bukatar ga shugaban kasa.

Daliban guda Uku sun yi amfani da wayar su ta salula ne inda suke raha ga Kungiyar Boko Haram, abinda jami’an tsaro suka yi amfani da shi wajen gurfanar da su a gaban kotu, aka kuma daure su.

Tuni dai daliban suka daukaka kara, kuma ana saran fara sauraron karar a watan Yuni mai kamawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.