Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya da Libya sun samu sassauci a OPEC

Najeriya da Libya sun samu sassauci daga matakin OPEC na rage yawan man da ake fitarwa a kasuwannin duniya domin farfado da farashin danyen mai da ya yi faduwar da ba a taba gani ba.

Karamin Ministan Fetir na Najeriya kuma shugaban kungiyar OPEC Ibe Kachikwu taron Vienna
Karamin Ministan Fetir na Najeriya kuma shugaban kungiyar OPEC Ibe Kachikwu taron Vienna REUTERS
Talla

OPEC ta tsawaita yarjejeniyar rage yawan fitar da mai na tsawon watanni 9 matakin da ake fatar zai farfado da farashin danyen mai a kasuwar duniya.

Hakan dai na nufin matakin bai shafi Najeriya da Libya ba.

A jiya Alhamis ne OPEC ta amince da matakin a taron ministocin mai na mambobin kasashen da aka gudanar a hedikwatar kungiyar da ke birnin Vienna na Austria.

Najeriya da Libya sun samu sassaucin ne saboda man da suke fitarwa bai kai adadin wanda suka saba fitarwa, saboda dalilai na fashe fashen bututun mai yankin Neja Delta na Najeriya da kuma rikicin da Libya ke fama da shi.

Najeriya na fitar da gangan mai kasa da miliyan biyu a rana, adadin ta saba fitarwa a kasuwannin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.