rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Sudan ta Kudu Salva Kiir Riek Machar Hakkin Dan Adam

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sudan ta Kudu: Yunwa ta tilastawa 'yan gudun hijira satar abinci

media
Wasu 'yan gudun hijira daga Sudan ta Kudu bayan sun ketara cikin Uganda a kan iyakar Ngomoromo a yankin Lamwo da ke arewacin kasar Uganda a ranar 4 ga watan Afrilu. REUTERS/Stringer/File photo

Rahotanni daga Uganda sun ce, yunwa na tilastawa ‘yan gudun hijrar da suka tsere daga Sudan ta Kudu satar abinci daga al’ummar kauyukan arewacin kasar ta Uganda, wadanda su kansu abincin bai ishe su ba.


Mazauna kauyukan na arewacin Uganda, sun ce a lokuta da dama, sun sha kama 'yan gudun hijirar da laifin, satar musu abubuwan da suka hada da amfanin gona, da dabbobi, tun bayanda hukumar da ke lura da wadatar abinci ta duniya WFP ta rage yawan kason abincin da take bai wa ‘yan gudun hijirar da misalign kilo 12 na masara zuwa kilo 6.

Jami’an da ke lura da sansanonin ‘yan gudun hijirar sun ce zuwa yanzu ba’a samu wani tashin hankali ba sakamakon satar da yan gudun hijirar ke yi wa kuyawan na Uganda.

‘Yan gudun hijira sama da 875,000 ne suka ketara kasar Uganda daga Sudan ta Kudu, tun bayan barkewar yakin basasa a kasar, cikin shekara ta 2013, tsakanin mayakan tsohon mataimakin kasar Riek Machar, da kuma sojin gwamnatin shugaban kasa Salva Kiir, wanda a yanzu ya koma fada na kabilanci.