Isa ga babban shafi
Nijar

Kashe wutar Libya zai yi maganin ‘yan ta’adda- Issoufou

Shugaban Jamhuriyar Nijar Issoufou Mahamadou daya daga cikin shugabannin Afirka da aka gayyata a taron G7 ya bukaci kasashen duniya su mayar da hankali wajen kokarin wanzar da zaman lafiya a Libya.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da shugaban Nijar  Mahamadou Issoufou a taron G7 da aka gudanar a Italiya
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da shugaban Nijar Mahamadou Issoufou a taron G7 da aka gudanar a Italiya REUTERS
Talla

Daya daga cikin batutuwan da taron shugabannin kasashen duniya bakwai masu karfin tattalin arzikin duniya ya tattauna a kasar Italiya shi ne fada da ta’addanci musamman mayakan IS da suka samu gindin zama a Syria da Iraqi da Libya.

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou ya shaidawa taron kasashen na G7 cewa yaki da ta’addanci a kasashen arewacin Afrika na bukatar tabbatar da zaman lafiya a Libya.

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Nijar Ibrahim Yacouba ya shaidawa RFI Hausa cewa akwai bukatar shigar kasashen duniya domin warware rikicin kasar ta Libya.

Shugabannin kasashen na G7, sun bukaci a hau teburin sulhu tare da taron sasantawa na kasa domin tabbatar da zaman lafiya tsakanin bangarorin da ke rikici a Libya.

Kasar Libya ta fada rikici tun kawar da gwamnatin Kanal Ghaddafi. Kuma kasashen Amurka da Faransa da Birtaniya na ci gaba da fuskantar suka kan yadda suka taimaka wajen kawo karshen gwamnatin Ghaddafi ba tare da yin wani tanadi ba akan makomar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.