Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Sojin Sudan ta Kudu 13 sun gurfana a gaban kotu

Jami’an sojin kasar Sudan ta Kudu 13 sun bayyana a gaban kotun sojoji da ke babban birnin kasar Juba, inda aka fara sauraron shara’ar zargin da ake musu, na yi wa wasu jami’an bada agaji biyar fyade, da kuma kashe abokin aikinsu.

Sojin Sudan ta Kudu da ake zargi da yi wa wasu jami'an bada agaji biyar fyade, tare da kashe wani abokin aikinsu.
Sojin Sudan ta Kudu da ake zargi da yi wa wasu jami'an bada agaji biyar fyade, tare da kashe wani abokin aikinsu. REUTERS/Jok Solomun
Talla

Hankula a yanzu sun karkata zuwa dakon ganin yadda wannan shari’ah zata kaya, wadda kma zata zama ma’aunin da za’a tantance kokarin cika alkawarin da gwamnatin Salva Kiir ta dauka na kawo karshen aikata laifukan yaki da sojin kasar ke yi.

Harin da aka bayyana shi a matsayin daya daga cikin mafi muni da aka taba kai wa kan ma’aikatan bada agaji a Sudan ta Kudu, ya auku ne a ranar 11 ga watan Yulin shekara ta 2016, lokacin da sojin kasar suka samu nasarar murkushe mayakan da ke biyayya ga tsohon mataimakin Shugaban kasar Riek Machar a birnin Juba.

Shaidun gani da ido sun yi wa kamfanin dillancin labarai na Reuters karin hasken cewa, a waccan lokacin, sojojin dauke da manyan makamai, sun kutsa kai ne cikin wani Otal mai suna Terrain da ke birnin Juba, inda suka shafe awanni suna aikata ta’asar, kafin su fice daga bisani, ba kuma tare da an kai wa ma’aikatan bada agajin taimako ba.

A waccan lokacin dai an tube shugaban sojin da ke aikin wanzar da zaman lafiya a yankin, yayinda kuma wanda gwamnati ta nada don lura da ayyukan sojin ya ajiye aikinsa sakamakon aukuwar mummunan al’amarin.

Majalisar Dinkin Duniya, da kuma kungiyoyin kare hakkin dan adam sun dade suna zargin bangaren sojin Sudan ta Kudu da na ‘yan tawaye, da aikata laifukan yaki, da suka hada da azabtarwa, kisan gilla da kuma aikata fyade.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.