Isa ga babban shafi
Nijar

Nijar: An tasa keyar Abdou Labo da matar Hama gidan yari

Mutane fiye da 20 da kotun Jamhuriyar Nijar ta sama da laifi a cinikin jarirai da aka ce an shigo da su daga Najeriya, an fara rarraba su a gidajen yarin kasar domin fara wa’adinsu na zaman gidan kurkuku.

Hama Amadou, da ke gudun hijira a Faransa na cikin wadanda kotu ta dare a Nijar
Hama Amadou, da ke gudun hijira a Faransa na cikin wadanda kotu ta dare a Nijar ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Daga cikin wadanda aka daure har da matar jagoran ‘yan adawar kasar Hama Amadou wadda aka kai gidan yarin Kollo, sai kuma tsohon ministan aikin gona na kasar Abdou Labo wanda aka wuce da shi zuwa gidan yarin Say garuruwan da ba su da nisa da Yamai fadar gwamnatin kasar.

A watan Maris aka yanke wa mutanen kimanin 20 hukuncin daurin shekara guda a gidan yari bayan kama su da laifin fataucin jarirai daga Najeriya ta hanyar Benin.

Jagoran adawa Hama Amadou na cikin mutanen 20 da aka yanke wa hukuncin daurin shekara guda a gidan yari duk da cewa ba ya cikin kasar.

A ranar 16 ga watan Maris na bara ne aka garzaya da Hama zuwa Asibitin Faransa daga gidan kaso a yayin da ya rage kwanaki a gudanar da zabe zagaye na biyu tsakanin shi da Shugaba mai ci Mahamadou Issoufou.

‘Yan adawa sun kauracewa zaben saboda rashin sakin Hama, tare da yin watsi da sakamakon zaben da Issoufou ya lashe da sama da kashi 92.

Hama Amadou babban mai adawa da shugaba Issoufou ya fice Nijar ne a watan Agustan 2015 bayan majalisa ta amince a kaddamar da bincike akansa game da badakalar mallakar ‘ya'ya ba bisa ka’ida ba da aka yi wa Matarsa fataucinsu daga Najeriya ta hanyar Cotonou.

Hama Amadou ya musanta zargin wanda ya danganta a matsayin yarfen siyasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.