Isa ga babban shafi
Tunisia

Ramadan: Tunisia ta daure mutane 4 da suka ci abinci a rana tsaka

Wata kotun Tunisia ta daure wasu mutane hudu na tsawon wata guda a gidan yari bayan sun ci abinci a bainar jama’a da rana tsaka a yayin da ake azumin Ramadan.

Al'ummar musulmi na buda baki a wani Masallacin Ahmedabad a India
Al'ummar musulmi na buda baki a wani Masallacin Ahmedabad a India REUTERS
Talla

An kama mutanen ne suna cin abinci da zukar taba a wani wajen shakatawa a birnin Tunis.

Mai Magana da yawun kotun Chokri Lahmar ya shaidawa Kamfanin dillacin labaran Faransa cewa mutanen hudu na da damar daukaka kara akan hukuncin cikin kwanaki 10.

Wuraren abinci dai sukan kasancewa a rufe a sassan Tunisia a lokacin Azumi, duk da cewa babu wata doka a kundin tsarin mulkin kasar da ta haramtawa mutane cin abinci a bainar jama’a a lokacin azumi.

Batun dai na ci gaba da janyo cece kuce a kasa, inda yanzu haka wasu mutanen Tunisia suka shirya gudanar da zanga zanga domin kare ‘yancin wadanda ba su azumin Ramadan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.