rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kwamitin Majalisa ya bayar da shawarar kara farashin man fetur

media
Zauren majalisar dattawan Najeriya venturesafrica

Kwamitin kula da ayyuka a Majalisar Dattawan Najeriya ya bukaci a kara farashin litar man fetur daga Naira 145 zuwa Naira 150, inda za a yi amfani da kudaden domin zubawa a wani asusun gini da kuma gyara hanyoyi a kasar.


Shawarar da kwamitin ya bayar ta zo ne shekara daya bayan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kara kudin mai daga Naira 87 zuwa 145.

A jiya alhamis ne ya kamata Majalisar ta tattauna kan rahoton da wannan kwamiti da ke karkashin jagorancin Sanata Kabiru Gaya ya gabatar, to sai dai an dakatar da har zuwa wani lokaci da ba a bayyana ba nan gaba.

Kwamitin ya bayar da shawarar yin Karin Naira 5 akan kowace lita daya ta mai da kuma dizal da aka shigo da shi daga waje ko kuma wanda aka tace a cikin gida domin zubawa a asusun gyaran hanyoyi, kuma 12 daga cikin mambobin kwamitin 15 sun amince da matakin.