Isa ga babban shafi
Nijar

Matsalar tsaro ta kara tsananta a iyakokin Nijar da Mali

Masana sha’anin tsaro na ganin cewa dole ne sai al’ummar Nijar sun tashi tsaye haikan tare da bayar da tasu gudunmuwa domin magance matsalar rashin tsaro da kasar ke fama da ita.

Niger-caserne-militaire
Niger-caserne-militaire © AFP PHOTO / BOUREIMA HAMA
Talla

A cikin watannin baya-bayan nan ana yawan samun hare-haren ta’addanci a yankin yammaci da arewacin kasar da suka yi iyaka da kasar Mali, inda a ranar larabar da ta gabata wasu ‘yan bindigar suka kai hari tare da kashe jami’an tsaron kasar shida a garin Abala da ke kusa da iyaka da Mali.

Kwanaki hudu kafin faruwar lamarin, wasu ‘yan bindigar sun kai hari tare da kashe ‘yan sanda biyu da wani farar hula daya a yankin iyakar kasar da Mali.

Hare-haren na faruwa ne duk da cewa akwai dubban sojojin kasashen Amurka, Faransa da kuma Jamus da aka jibge domin dafa da ayyukan ta’addanci a kasar ta Nijar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.