Kasashen Sahel na bukatar Kudi Euro miliyan 50 daga Tarayyar Turai don yakar masu tsananin kishin Islama
Kasashen Sahel da ke yammacin Africa sun roki Tarayyar Turai da ta kai ma su dauki na kudaden da suka kai kudin Turai Euro miliyan 50 domin a samu a biya hakkokin Dakarun karo-karo da ke yakar masu tsananin kishin Islama da ke yankin.
Wallafawa ranar:
Babban Hafsan Sojan Mali Janar Didier Dacko ya gabatar da wannan bukata a yau Asabar wajen taron manyan sojojin da ke yakar masu tsananin kishin Islaman.
Yankin na Sahel da suka hada da Chadi, Nijar, Burkina Faso , Mali da Mauritania sun kasance makwancin masu tsananin kishin Islama, dake hana sakat a yankin.
Babban Hafsan ya fadi a wajen taron Hafsoshin sojan kasashen biyar cewa suna bukatar kungiyar Tarayyar Turai ta kai masu tallafi.
Gobe lahadi ne kuma Ministocin tsaro na kasashen za su yi nasu taron.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu