rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Mali Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Rundunar Sojin Barkhane ta kashe yan tawaye arewacin Mali a dajin Serma

media
Dakarun dake yakar yan tawayen arewacin Mali a kan iyaka da Nijar ISSOUF SANOGO / AFP

Rundunar Barkhane dake dafawa kasashen Sahel a yakin da suke da yan tawaye sun samu nasarar kashe wasu yan tawayen arewacin Mali 20 a wani farmakin da suka kaddamar zuwa dajin Serma dake da nisan kilometa kusan 200 kudu maso yammacin garin Gao.


Rahotanni daga rudunar ta Barkhane na nuni cewa daga ranar 28 ga watan yuni da ya shude ne Sojojin kawance na rundunar suka kasance cikin shiri a kokarin sun a kawo karshen yan tawayen arewacin Mali dake ci gaba da kawo fargaba a zukatan jama’a.