rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Morocco ECOWAS CEDEAO

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sarkin Morocco ba zai halarci taron Ecowas

media
Sarkin Morroco Muhammad na shida

Sarki Morocco na shida ba zai halarci zaman taro na 51 na kungiyar Ecowas da zai gudana a kasar Liberia daga ranar 3 zuwa 4 ga wannan watan da muke ciki.


Fadar sarki Mohamed na shida ta futar da sanarwa dake zuwa a dai dai lokacin da ake gab da bude zaman taron na yau a birnin Moronvia na kasar ta Liberia.
Kauracewa taron na Ecowas na zuwa ne bayan da Firaministan Isra’ila Benjamin Nethanyahu ya sanar da cewa zai halarci zaman taron .
Ana zaman doya da man ja tsakanin Isra’ila da Morocco, haka zalika wasu kasashen sun sanar da turo wakilan su a taron na Ecowas.