rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Sudan ta Kudu

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Yara 15 ne suka mutu bayan wata alura a Sudan ta kudu

media
Wani sansanin 'yan gudun hijira da ke Sudan ta kudu Beatrice Mategwa/United Nations Mission in South Sudan (UNMISS)

Yara  15 ne aka bayyana mutuwar su bayan da aka yi masu alura ta yaki da kamuwa da cutar dusa mai dauke da guba a wani yanki mai suna Kapoeta na kasar Sudan ta kudu.
 


Ministan kiwon lafiya na kasar ta Sudan ta kudu Riek Gai Kok a wata ganawa da manema labarai a Juba dake babban birnin kasar ya bayyana cewa binciken farko daga kwarraru tareda hadin guiwar ma’aikantan kiwo lafiya na hukumar lafiya ta Duniya na tabbatar da cewa an yi amfani da alura daya wajen yiwa ilahirin yara shau’shawa, banda haka babu kyaukiyawar kulawa dama tsapta a lokacin.