rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Afrika Tarayyar Turai Ta'addanci Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Afrika: Kasashen yankin Sahel sun nemi tallafin Euro miliyan 50 daga EU

media
Hoton tambarin rundunar sojin Barkhane sanye jikin wani jami'in sojan kasar Faransa, a yankin Gao dake arewacin kasar Mali. REUTERS/Christophe Petit Tesson/Pool

Babban hafsan sojin kasar Mali, Didier Dacko, ya ce kasashen yankin Sahel na yammacin Afrika, na bukatar tallafin akalla Euro miliyan 50, daga kungiyar tarayyar turai EU, domin kafa rundunar soji ta hadin gwiwa, da zata murkushe barazanar da ‘yan ta’adda ke yi a yankunan kasashen da ke yankin na Sahel.


Dacko ya bayyana bukatar ce, yayin wani taro da ya gudana a babban birnin Bamako, Mali, tsakanin manyan hafsoshin sojin kasashen G5, wakilan kungiyar tarayyar turai EU, da kuma wasu manyan jami’an sojin kasar Faransa.

Tun a baya ne dai kasashen na G5, da suka hada da Chadi, Nijar, Burkina Faso, Mali da kuma Muritania, suka amince da kafa rundunar sojin, don kawo karshen ayyukan ta’addancin, sai dai matsalar kudi ta hana aiwatar muradin.

A ‘yan shekarun da suka gabata dai, kungiyoyi masu da’awar jihadi suna amfani da yankin na Sahel wajen horar da mayaka, da kuma kai farmaki, a wasu sassa, a kokarinsu na mamaye yankuna da dama musamman ma a kasar Mali.

Masana na ganin kafa sabuwar rundunar a matsayin taimako ga dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya, da kuma akalla sojojin Faran 4,000 da kasar da girke a tsakanin kasashen biyar na yankin Sahel.

Ko a ranar Juma'ar da ta gabata,Ma'ikatar tsaron kasar Faransa ta sanar da samun nasarar kashe wasu mayakan jihadi 20, a kasar ta Mali.