rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Afrika Guinea Conakry Muhalli

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

AU ta jaddada manufar mutunta yarjejeniyar rage dumamar yanayi

media
Hedikwatar kungiyar tarayyar nahiyar Afrika AU a birnin Addis Ababa na kasar Habasha. REUTERS/Tiksa

Kungiyar tarayyar nahiyar Afrika AU, ta bayyana cikakken goyon bayanta ga yarjejeniyar rage dumamar yanayin da aka cimma a birnin Paris, na kasar Faransa


Jagoran kungiyar a yanzu kuma shugaban kasar Guinea Alpha Conde, yayi ala wadai da watsin da shugaban Amurka Donald Trump yayi da yarjejeniyar a ranar Alhamis da ta gabata.

Zalika cikin jawabin da ya gabatar, Conde, ya bukaci da a sake tattaunawa kan batun rage dumamar yanayin, a taron kasashen G20 da za’a yi, a watan gobe, wanda kasar Jamus zata karbi bakunci.

A cewarsa, ko da ya ke, kasashen nahiyar Afrika basa taka muhimmiyar rawa wajen gurbata yanayi, a bayyane ta ke, nahiyar na kan gaba, a tsakanin yankunan duniya da illar dumamar yanayin ta fi shafa.