rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kamaru BOKO HARAM Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kamaru ta tsare sojojin da ke yaki da Boko Haram

media
Wasu daga cikin sojojin Kamaru da ke yaki da Boko Haram AFP PHOTO / REINNIER KAZE

Hukumomin Kamaru sun kama akalla sojoji 30 da ke yaki da kungiyar Boko Haram saboda boren da su ka yi kan kin biyan su wasu kudade na alawus da na hutu.

 


Sojojin sun yi bore a ranar Lahadin da ta gabata a yankin arewacin kasar, in da suka tare hanyoyin zirga-zirgar mota.

Ma’aikatar tsaron kasar ta ce, yanzu haka an kwashe sojojin daga yankin Zique zuwa birnin Yaounde, in da ake tsare da su.

Rahotanni sun ce, harkokin yau da kullum sun koma yadda aka saba bayan boren sojojin.