rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Rahotanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Wasu kungiyoyin matasan Arewa sun bukaci a raba Najeriya

media
Birnin Kaduna a arewacin Najeriya jujufilms.tv

Wasu gamayyar kungiyoyin matasan Arewacin Najeriya a Kaduna sun bukaci a gudanar da zaben raba gardama domin raba Najeriya tare da yin gargadi ga ‘yan kabilar Igbo da ke fafutikar kafa kasar Biafra.


Matasan sun ce sun dauki wannan matsaya ce sakamakon yawan rikice-rikice masu nasaba da shelanta ballewar yankin Biafra da ‘yan kabilar ta Igbo ke yi daga Najeriya.

Amma gwamantin jihar Kaduna ta bayar da umurnin kama shugabannin kungiyoyin matasan 16 wadanda suka fitar da wata sanarwa da ke gargadin ‘yan kabilar Igbo su bar yankin na arewa a cikin watanni uku masu zuwa.

Ga dai rahoton da wakilinmu Aminu Sani Sado ya aiko daga Kaduna.

Wasu kungiyoyin matasan Arewa sun bukaci a raba Najeriya 07/06/2017 - Daga Aminu Sani Sado Saurare