Isa ga babban shafi
Chadi

Chadi ta kira jekadanta daga Qatar

Gwamnatin kasar Chadi ta kira jakadanta a kasar Qatar da ya koma gida don a tattauna da shi sakamakon rikicin da ya barke tsakanin kasar Qatar da kasashen Larabawa.

Shugaban Chadi Idriss Déby
Shugaban Chadi Idriss Déby REUTERS/Alain Jocard
Talla

Chadi ta bi sahun sauran kasashen Afrika da suka janye jekadansu daga Qatar domin nuna goyon baya ga Saudiya.

Kasar Senegal ta gayyaci jakadanta ya koma gida, yayin da kasar Mauritania da ke cikin kungiyar kasashen Larabawan ta janye jakadanta daga Qatar.

Tuni Masar da Gabon suka janye jekadunsu daga Qatar.

Wata sanarwa daga Gwamnatin Chadi ta nanata bukatar ganin an warware takaddamar da ke tsakanin kasashen na Larabawa maimakon kai ruwa rana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.