rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kamaru Hakkin Dan Adam

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kamaru ta tsare shugabannin masu magana da harshen Ingilishi

media
Ana yawaita samun rikici a yankin masu amfani da harshen Ingilishi a Kamaru

Wata Kotun Soji a kamaru ta tsare wasu shugabannin Al’ummah da ke yankin masu Magana da harshen Ingilishi saboda zargin su da shirya ayyukan ta’addanci.


Kotun da ke zamanta a Younde ta tsare Lauya, Felix Agbor Nkongho, da Malamin Makaranta Neba Fontem Aforteka’a da kuma Mancho Bibixy ma’aikacin gidan Radio.

Majiyoyi na cewa kotun Sojin ta ki bada belinsu kafin ranar 29 ga wannan wata da za’a koma kotun.

Kazalika ta ki amincewa ta bada belin wasu mutanen 24 da aka kama ana tsare da su saboda zargin ayyukan ta’addanci.

Dukkannin wadanda ake zargi hukuncin su kisa ne.

Bernard Muna auya da ke kare wadanda ake zargin ya shaidawa kamfanin dilancin labaran Faransa, AFP, cewa bai ji dadin matsayin kotun ba.

Tun a watan Janairu ne dai, ake tsare da su a lokacin da wata kungiya ta kira zanga-zanga don a goyi bayan neman hakkin amfani da harshen Ingilishi, a inda ake da masu Magana da harshen su kimanin kashi 20% na Al’ummar kasar miliyan 22.