Isa ga babban shafi
Najeriya

Ana bukatar makuddan kudin don farfado da matatun man Najeriya

Karamin minista a ma'aikatar mai ta Najeriya Dr Ibe Kachikwu, ya ce ana bukatar dala milyan dubu daya da milyan 200 domin tabbatar da cewa matatun mai uku na kasar sun koma aiki kamar yadda ake bukata.

Ministan mai a Najeria Ibe Kachikwu na magana a birnin Vienna
Ministan mai a Najeria Ibe Kachikwu na magana a birnin Vienna REUTERS
Talla

Kachikuwa ya ce matukar ba a samar da wadannan kudade ba, zai kasance abu wuya matatun kasar da ke Port Hacourt, Warri da kuma Kaduna su koma aiki kamar yadda ake bukata, inda ya musanta bayanan da ke cewa gwamnati ta sayar wa wasu kamfanoni hannayen jarin wadannan matatu.

Ministan ya ce babu gaskiya a game da jita-jitar da ke cewa gwamnati ta mika lamarin tafiyar da matatar Port Hacourt a hannun kamfanin Agip reshen ENI na kasar Italiya ko kuma kamfanin Oando da ke Najeriya.

Minista Kachikwu ya musanta wannan jita-jita ce lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan ya gana da 'yan majalisar dattawan kasar a birnin Abuja.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.