rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shirin samar da wutar lantarki a jamhuriyar Nijar

media
Turken wutar lantarki

A jamhuriyar Nijar kamfanin gine-gine na Sogea-Satom wanda ya share sama da shekaru 50 yana aiki a cikin kasar, karon farko ya samu kwangila a bangaren da ya shafi wutar lantarki a kasar.


Satom mallakin ‘yan kasuwar Faransa, ya kulla yarjejeniya da wani kamfani mai suna L.S.E de Vinci Construction International Network wanda ya shahra ta fannin ayyukan wutar lantarki domin aiwatar da wannan kwangila da ya sama akan kudi Euro milyan 9.

Hukumar raya kasashe ta Fransa, Agence Francaise de Developpement ce ta bayar da wadannan kudade, domin fadada aikin samar da wutar lantarki a birnin Yamai fadar gwmanatin kasar ta Nijar.

A karkashin wannan kwangila, Satom za ta kafa manyan turakun wutar lantarki na karfe da ake kira Moyenne Tension tsawon kilomita 35, sai kuma kashi na biyu da ake kira Reseaux basse tension tsawon kilomita 455, tare da kafa wasu manyan na’urorin wutar lantarki domin kamfanin kasar ta Nijar mai suna Nigelec.