rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya BOKO HARAM

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An zartar wa Sojan Najeriya hukuncin kisa

media
Sojojin Najeriya da ke fada da Boko Haram AFP PHOTO/SUNDAY AGHAEZE

An zartarwa wani Sojan Najeriya hukuncin kisa bayan kama shi da laifin kisan wani da ake zargin dan Boko Haram ne a Damboa Jihar Borno. Akwai kuma wasu sojoji guda 4 da aka yanke wa hukuncin dauri a gidan yari.


An bayyana sojan a matsayin Koforal Hilary Joel wanda kotun soji ta zartarwa hukuncin kisa a yau Juma'a.

Babu dai wani cikakken bayani akan yanayin kisan da sojan ya aikata akan dan Boko Haram.

Akwai wasu sojoji guda 4 da aka yanke wa hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari kan taimakawa wajen kisan mutane a Maiduguri.

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama dai sun dade suna zargin sojoji da wuce gona da iri wajen kisan fararen hula da sunan yaki da Boko Haram